SAKON GWAMNAN NASARAWA GA MUTANIN PLATEAU -KADA KUYARDA YAN SIYASA SU HADDASA GABA DA KIYAYYA A TSAKANINKU.

SAKON GWAMNAN NASARAWA GA MUTANIN PLATEAU
-KADA KUYARDA YAN SIYASA SU HADDASA GABA DA KIYAYYA A TSAKANINKU.

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya jajantawa takwaransa na jihar Filato, Gwamna Simon Bako Lalong, da kuma mutanen jihar, kan rikicin baya -bayan nan da ya haddasa asarar rayuka da asarar dukiya na miliyoyin nairori.

Gwamna Sule, ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagar manyan masu fada aji daga jihar Nasarawa tare da sashin Shugabaninnin addinai zuwa gidan Gwamnatin dake garin Jos.

Yayin da yake nuna damuwa kan abin da ya faru a jihar Filato kwanan nan, Gwamnan ya ce ya kai ziyarar ne cikin yanayin ‘yan uwantaka da hadin kai, tare da sanin Gwamna Lalong da jama’ar jihar, musamman a irin wannan lokacin da jihar tashi halin damuwa.

Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ke kokarin lalatan zaman lafiya da aka samu a jihar Filato. Da dangan takar dake tsakaninsu.

A cewar Gwamnan, zaman lafiya ya kasance mafi inganci ga kowane irin cigaba, yana mai jaddada cewa matukar babu zaman lafiya, ba za a samu cigaba ba a tsakanin al’umma.

Ya yaba wa Gwamna Lalong kan kokarinsa na dawo da zaman lafiya da cigaba, ba ga jihar kadai ba har ma da Arewa baki daya, a matsayinsa na shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF).

Injiniya Sule ya ce ya ga ya zama dole ya jagoranci wannan ziyara saboda tarihin mutanen jihohin biyu, ya kara da cewa mutanen Nasarawa ba za su iya jingina hannayensu ba, da zarar an samu rikici a jihar Filato.

Ya kuma roki mutanin jihar da su yi hakuri da junansu, ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini ba, musamman cewa babu wani daga cikin manyan manyan addinan biyu da ke yarda da kashe -kashe ko lalata dukiya.

Gwamnan ya yi kira ga mutanen jihar Filato da kar su yarda ‘yan siyasa su raba dangantakar dake tsakanin su ta hanyar cusa gaba da kiyayyan juna a zukatansu.

Ya rikosu da su dawo cikin hankalinsu su zauna lafiya da junansu, su sani basu da wata jiha da tawuce jihar Filato.

Ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da na addini, kan muhimmiyar rawar da suke takawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

A nasa jawabin Gwamnan jihar Filato, Rt. Hon Simon Bako Lalong, ya godewa takwaransa na jihar Nasarawa da ya kai ziyarar, domin nuna goyon baya da hadin kai ga Gwamnati da mutanen jihar Filato.

Ya kara da cewa, Filato gida ce ga mutanen jihohin Nasarawa da Binuwai, Lalong ya yi godiya ta musamman ga Injiniya Sule, kan nuna damuwar sa tun lokacin da rikicin ya barke.

Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin sa tana aiki tukuru don magance matsalolin da ke haifar da rikicin akai -akai.

A cewar Gwamnan jihar Filato, tsaro shine yadda mutanen jihar za su iya zama tare cikin lumana, ya kara da cewa, lokacin da mutane suka kasance masu hadin kai kuma suka yarda a zauna lafiya, ba za a sami rikici ba.

Hakanan, a wani bangare na ziyarar, gwamnonin biyu sun shiga wata ganawar sirri da shugabannin gargajiya da na addini daga jihohin Filato da Nasarawa, da nufin tabbatar da dawwamammen zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *