An yabawa yan Jarida wajen binciko yadda ake cin zarafin mutani a sassan Afirka

An yabawa yan Jarida wajen binciko yadda ake cin zarafin mutani a sassan Afirka

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Kungiyar BRCI tayi wani bincike kan wani yaro a garin Calabar dake Jihar  Cross-River  wanda yanzu haka yana hannun Yan Sanda bayan kubutoshi daga wani garkamiwar da akayi masa na tsawan lokaci a wani gida.

Yan Jaridu sun binciko dalilin garkame wannan yaro sakamakon ya karya dokar da aka gindaya masa.

Shugaban kungiyar BRCI Mr.kebe ikpi; ya yabawa kokarin yan jarida yadda suke zakulo ire-iren wannan cin zarafin suke nunawa a Duniya.

Hukumar kare hakin Bil- Adama tana nuna damuwa matuka kan yadda ake cin zarafin mata ko yara qanana.

Yace; wani lokacin idan yan Jarida suka kawo irin wannan Labarin sai kaga abin tausayi kamar ba mutum ne da iyaye suka haifaba akeyima haka.

Mr. kebe ikpi  yayi kira ga Kungiyoyin addinai dana gargajiya da hukumomi kan su rika wayarma Iyaye da Jama’a da kai domin dakile irin wannan hukunci ko cin zarafin mutani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *