Duba rayuwar al’umman Arewa maso gabas shiyafi mahimmanci – Mista Edward Kallon

Duba rayuwar al’umman Arewa maso gabas shiyafi mahimmanci – Mista Edward Kallon

Daga Zubairu Lawal

Miliyoyin mutane suna cikin matsala rayuwa a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya suna gab da afkawa cikin matsalolin yunwa da muguwar Talauci, duba da yadda yanayin ya kasance na rashin ingantacen zaman lafiya da al’umman yankin zasu gudanar da Noma domin samun abinci mai gina jiki da harkan kasuwanci na saya da saidawa.

Idan ba’a kawo agajin gaugawa a jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe ba , miliyoyin mutane ka iya fuskantar matsanancin wahala wajen ciyar da kansu a shekarar 2021.

Kamar yadda hukumar Cadre harmonise food ta fitar a watan March, 2021 , akalla mutane miliyan 4.4 , hadda wanda rikici ya barosu daga gidajensu  zasu fuskanci karancin abinci.

Wasu mutanen da akalla su kusan dubu 775,000 suna cikin matsala na rashin abinci , shine mafi muni a shekaru 4 daya gabata.

Masu jinkai na (UN) da kuma kungiya masu Zaman kansu sun hada hannu wajen ganin sun kawo karshen matsalar rashin abinci a Arewa maso gabas dake tarayyar Najeriya.

Mr Edward kallon shine maisa ido na jinkai ya fitar da wani sanarwa kan wasu yara na wanda ke kuka a cikin dare saboda yunwa,  mista kallon yace wasu magidanta suna fama da karancin abincin da zasu iya ciyar da yayansu, gashi ba ruwa  mai kyau, ba tsaftace muhalli  kuma ba isasshen lafiya.

Ya kara da cewa ya kamata kungiyoyin sa kai da masu hannu da suni da Gwamnatoci su kara kaimi kan kokarin da akeyi na taimakawa al’umman wannan yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *