Dubban matasa a Nijeriya na fama da rashin aikinyi – Jane

Dubban matasa a Nijeriya na fama da rashin aikinyi – Jane

Daga Zubairu Lawal

Mani matashi mai sana’ar yanar gizo ya koka da halin da Dubban matasa ke fama dashi na rashin aikinyi a Nijeriya.
Jane matashine mai matsakaicin shekaru da bai wuce 24 ba, yace;halin da ake ciki na rashin aikin yi ya jefa Dubban matasa cikin aikin rashin gaskiya.

Jane yace yayi kokari ya koyi Sana’ar yanr gizo domin rufawa kansa asiri.

Yace a yanzu yana  horarsa da matasa hanyar da zasubi don ganin samu kudi mai kyau ta yanar gizo, cewar Jane. Matasa sun cigaba da nuna kwazonsu Dan samarwa kansu da mafita saboda halin rayuwa da ake ciki.

Kamar “Ni Jane na samu kaina cikin wani Hali amma nayi kokari na gina kaina” .

. kungiyar ILO tace  , matasa masu aikinyi ya ragu da kashi 8.7 a 2020 , kaso 3.7 duk maza balagaggu ne, saboda halin da kasar ta tsinci kanta a rashin kudi. Matasa a Najeriya suna Kira da shugabanninsu da kuma Gwamnati da tayi tsari wanda zai rage halin da matasa ke ciki da kuma yadda za’a gina matasa.

Misis.Ezekiel   Aina  Tace akwai tazara mai yawa ta yadda zaayi kokarin gina matasa a wannan kasar.tayi  kira da babban murya kan cewa gwamnati da kuma shugaba masu amfani su taimaka wajen koyar da matasa hanyar samun kudi ta intanet da kuma kwasa-kwasai ta yanar gizo don ganin ya Samar masu da aiki.

Ezekiel Aina tace  raayoyin matasa a wani zabe da aka gudanar ya nuna cewa dubban matasa wanda suke shekara 14-2 a wajen zaben kaso 48 ne.

Yayin da abin da akafi jin tsoro shine matasan Najeriya basu da aikinyi , kaso 30 sunce sanaar yanar gizo shine wanda yafi dacewa a koya , wasu kaso 44 sunce gina wasu wajen sana’o’i don koyar da Sanaa  zai karafafa da kuma shawo kan matsalar da matasan Najeriya ke ciki na rashin aikinyi a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *