Yan Ta’adda bazasu samu mafaka a jihar Nasarawa ba  Inji Gwamna Abdullah Sule

Yan Ta’adda bazasu samu mafaka a jihar Nasarawa ba
Inji Gwamna Abdullah Sule

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnatin jihar Nasarawa ta dauki kwararan matakai na dakile hanyoyin da miyagu zasu shigo jihar.Gwamna Abdullahi Sule, ya ummurci dukkan vangarorin tsaro dake aiki cikin jihar dasu dauki matakai na kariya ga dukkan dazuzukan jihar saboda dakile yaduwar yan Ta’adda.

Gwamnan ya bayyana haka a taron vangaren tsaro a ranar Littinin a gidan Gwamnati. Yace;  barayin da ke tserewa a halin yanzu sakamakon  jerin hare -haren da sojoji a yankin Arewa maso Yamma ke kai masu ya sanya suke gudu zuwa wasu jihohin.

Gwamna Abdullah Sule ya yabawa shugaban qasa Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro kan  nasarorin da aka samu a yaki da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane a fadin qasa.

Gwamnan  ya nuna damuwa, kan yan fashin da ke tserewa, na iya neman mafaka a yawancin sassan wasu jihohin dake Arewacin, masamman idan akayi la’akari da kungiyar  Darussalam da abaya suka mamaye wasu sassan jihar Nasarawa.

Injiniya Sule ya ce akwai bukatar jihar ta dauki kwararan matakai, domin dakile wadannan barayin da ke tserewa daga jihohin da ake fatatakarsu domin niman  mafaka a jihar Nasarawa, tare da ba da kariya ga mutanen jihar.

Gwamnan ya ce ya zama wajibi ga membobin kwamitin tsaro, don tattauna yanayin tsaro a duk fadin qasar da yadda hakan ke shafar jihar Nasarawa.

Ya qara da cewa shigowar darussalam a shekarar 2018, lokacin da yan kungiyar da suka tsere daga jihar Neja, suka samu mafaka a cikin dazuzzukan na Qaramar hukumar Toto sun zamo barazana a jihar.

Ya nuna damuwar sa kan cewa nasarorin da aka samu a halin yanzu akan yan bindiga a Neja, Zamfara, Kaduna da sauran jihohin Arewa maso Yamma, na iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar Nasarawa.

Injiniya Sule ya jaddada cewa saboda haka ya zama dole, membobin majalisar su taru su yi dabaru, da nufin kare jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *