Sama da mutum 67000 ya jihar Borno Ke gudun Hijira a kasar Kamaro Inji Mista  Mazou

Sama da mutum 67000 ya jihar Borno Ke gudun Hijira a kasar Kamaro

Inji Mista  Mazou

Daga Zubairu .Lawal

Mista Mazou ya nuna damuwarsa kan yadda al’umman jihar Borno ke yaduwa a gurare dabam dabam ciki harda kasar ketare.

Yace sama da mutum 67,000 ya jihar Borno Ke gudun Hijira a kasar kamaru, wannan abin duba rayuwarsu ne.

Mista Mazou ya jinjinawa Gwamnatin jihar Borno kan yadda take bada kulawa ga al’umman dake rayuwa a sansanin yan gudun Hijira.

Yace; sanin kowane mutanin dake rayuwa a ire iren wadannan guraren suna da bukatar kulawa masamman a fanin ci da sha da Kuma vangaren kiwon lafiya.

Yace; mutanin dake rayuwa a sansanonin gudun Hijira mutanine da rayuwarsu take da mahimmanci na kawai sun sanya kansu ne na zama a nan ba,lalurace wanda kuma dole ya sanyasu suke rayuwa a wanan gurin.

Mista Mazou yace; kulawar da Gwamnati take baiwa yan gudun Hijira a fannin kiwon lafiya da al’amurar yau da kullun babban abin a yaba ne.

Yace; a kokarin Gwamnatin na maida yan gudun Hijira zuwa garuruwansu ayyukane na cigaba amma ba za a kammalashi a kan kanin lokaci ba.

Ya Kuma yabawa kungiyoyin dake bada gudumawa a sansanonin gudun Hijira dake yankunan da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *