Mata basu cin moriyar siyasa a Nijeriya- Jsohn Donnelly

Mata basu cin moriyar siyasa a Nijeriya Jsohn Donnelly,

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Jakadiyar qasar Australian a tarayyar Nijeriya Misis John Donnelly, ta bayyana damuwarta kan yadda mata basu samun mukamin zavevu a siyasan Nijeriya.

Tace; tsarin mulkin Nijeriya yaba mata damar tsaya takarar kowani mukami tundaga matakin kujerar Shugaban qasa zuwa Gwamna zuwa Sanata da yan Majalisa.

Amma abin bakin ciki a duk lokacin zave matan dake tsaya taka basu wuce kashe goma kacal. Kuma masu yin nasara a zave basu kaiwa kashe uku da digo takwas.

Tace ; sau dayawa mata sunfi maza fitowa kada kuri’a a dukkan zavuvukar Nijeriya. Amma ana samun karancin mata dake tsaya takarar zave.

Bugu da kari matan basu iya baiwa mata yan uwansu kuri’a mafi rinjaye.

Misis John Donnelly, ta bayyana hakane a wajen taron karawa juna sani da wayar da kai Wanda  sashin yada labarai na Majalisar Xinkin Duniya ta shirya a birnin Abuja cikin makon da ya gabata.

Tace ; mata suna samun moriya kadanne a siyasan Nijeriya bayan an kafa Gwamnati akan basu mukamai kasa da kashi goma sha shida, a cikin Gwamnati mai makon nasu yafi yawa ko ya zo dai dai.

Daga karshe an bukaci mata da su rika jurewa suna tsayawa takarar kujeru manya da qanana daga matakin Tarayya zuwa Jihar da qananan hukumomi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *