Zamuyi yaki da zaman kashe wando a Niger-Delta Inji Gwamnan Bayelsa

Zamuyi yaki da zaman kashe wando a Niger-Delta
Inji Gwamnan Bayelsa

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnan jihar Bayelsa Honarabul Douye Diri, yace tsarin Gwamnatinsa ta daurune kan yaki da zaman kashe wando ga matasan jiharsa.

Gwamnan yace samar da ayyukanyi ga matasa shine sahihin hanyar tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ga al’umman qasa.

Gwamna Douye Diri, na jihar Bayelsa ya bayyana hakane a taron koyar da sana’o’in hannu na dogaro da kai wanda Gwamnatin Tarayya da Kungiyar tarayyar Turai da Majalisar Xinkin Duniya suka gabatar a yankin Niger-Delta, Wanda ya gudana a Birnin Yenagoa shalkwatar Bayelsa.

Gwamnan yace; matasan yankin Niger-Delta hazikaine masu kaifin basira da hikima da ilumin zamani.

Wannan sana’ar zai kara bunkasa tattalin arzikin yankin Niger-Delta dama Nijeriya baki daya. Duk da cewa an samar da hadin giwa ne domin gudanar da wannan ayyukan bai daya na taimakawa matasa da sana’ar yi. Da gaske wannan zai sanya matasa su dogara da kansu su Kuma dauki nauyin kansu da iyalansu.

Ya qara da cewa kudurin Gwamnatin na yaki da talauci da zaman kashe wando da yaki da miyagun kwayoyi yana nan daram.

Kuma Gwamnatinsa zata cigaba da baiwa matasa fifiko a vangarori dabam dabam.

An zakulu. Matasan ne daga jihohin Bayelsa da Rives da Edo, yadda aka koyar dasu sana’o’i dabam dabam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *