Gwamnatin Nasarawa ta kaddamar da takin zaman kan 7,000

Gwamnatin Nasarawa ta kaddamar da takin zaman kan 7,000

Daga Zubairu M Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaddamar da sayar da takin zamani ga manoma domin noman rani na shekarar 2021/22,

Gwamnan ya gargadin jami’an da ke kula da rabon kayayyakin da sukula wajen rabawa manoma

Injiniya Sule ya kaddamar da sayar da takin da sauran kayayyakin amfanin gona, a biki da aka gudanar a hedikwatar shirin bunkasa noma na Nasarawa (NADP), a ranar Laraba.

A cewar Gwamna, Gwamnatinsa za ta cigaba da baiwa manoman jihar goyon baya domin ganin jihar Nasarawa ta cigaba da rike matsayin jihar a halin yanzu ta fuskar noman amfanin gona.

Yaca; Gwamnati ta sayi metric tonne 600 na buhun taki mai nauyin kilogiram 50 akan N9, 300 kan ko wace buhu amma za ta baiwa manoman tallafin naira 7,000 akan kowacce buhu.

Sai dai Injiniya Sule ya fusata kan yanayin da ake karkatar da takin da aka yi wa manoma ana sayar da shi a kasuwa.

Don haka ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da su hada kai da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, domin ganin an sayar da kayan ga manoma na gaskiya.

Ya kara da cewa, a wani hadin gwiwa da cibiyar binciken kayayyakin amfanin gona ta Najeriya (NSPRI), wacce ta samu horon zababbun ma’aikatan hukumar ta NADP kan sabbin fasahohi kan sarrafa bayan girbi.

Hakan ma ya kasance kamar yadda Hukumar Hadin Kan Kasa da Kasa ta Japan (JICA), ta ba da gudummawar famfunan ban ruwa 55 ga manoman noman rani 55 a cikin rukunoni uku a kwanan baya, domin bunkasa noma a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *