Jihar Nasarawa zata cigaba da daukar matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya – Gwamna Abdullahi Sule

Jihar Nasarawa zata cigaba da daukar matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya – Gwamna Abdullahi Sule

Daga Zubairu M.Lawal

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya kara jaddada aniyarsa na tabbatar da za!an lafiya mai dorewa a fadin Jihar .

Gwamnan ya bayyana hakane a taron masu ruwa da tsaki kan lamarin tsaro na jihar da yagudana a fadar Gwamnatin jihar ranar Laraba 5/1/2022.

Taron ya samu halartan Manyan jami’an tsaro da Sarakunnan Gargajiya da Shugabannin Kabilun da sukafi yawan samun sabani wato Fulani da Tiv.

Gwamna Abdullahi Sule, ya ce; ya zama dole mu duba rikicin baya-bayan nan da ya auku a sassan jihar, da nufin samar da matakan da suka dace domin dakile sake faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *