Real za ta san wadda za ta fuskanta a Copa del Rey ranar Juma’a

Real za ta san wadda za ta fuskanta a Copa del Rey ranar Juma’a

Daga Aliyu Mustapha

Ranar Juma’a 7 ga watan Janairu ake sa ran raba jadawalin wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar Copa del Rey ta bana.

Jadawalin da za a gudanar a hukumar kwallon kafar Sifaniya zai fayyace kungiyar da Real Madrid za ta fuskanta, bayan da ta yi waje da Alcoyana.

Watakila a hada Real da wata karamar kungiyar a zagayen gaba, wadda ta taka rawar gani a fafatawar kungiyoyi 32.

Wasu kungiyoyin da suka kai bantensu sun hada da mai rike da kofin, Barcelona da Espanyol da Real Sociedad da Mallorca da Valencia da Atletico Baleares da Betis da Rayo Vallecano da sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *