KUNGIYAR MATASA TA YAKIN NIMAN ZABEN YAHAYA BELLO TA BUDE OFISHINTA A JIHAR NASARAWA

KUNGIYAR MATASA TA YAKIN NIMAN ZABEN YAHAYA BELLO TA BUDE OFISHINTA A JIHAR NASARAWA

Daga  Zubairu Lawal

Duban matasa maza da mata sun gudanar da gangamin kira da babban murya ga Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello na ya fito ya tsaya takarar Shugabancin Nijeriya domin ceto kasar.

Taron da ya gudana a katafaren Ofishin wanda matasan suka gudanar da bukin budewa a harabar cibiyar kasuwanci na Kaura Plaza dake garin Lafia.

Da yake jawabi Shugaban kungiyar yakin gangamin niman takarar Gwamna Yahaya Bello, Alhaji Ibrahim L. Ibrahim. Yace; wannan gangamin da mukeyi a matsayinmu na matasa, muna kirane ga Matashin Gwamna mai jini a jika cewa wannan lokacin matasa sun lura Nijeriya na bukatar jajirtatcen Shugab kuma matashi, wanda zai daura bisa ga kokarin da Shugaba Muhammad Buhari yayi.

Yace; Yahaya Bello jarumin Gwamnane, wanda ya cancanci Shugabanci da sanin ya kamata. Yace ; idan Yahaya Bello ya zama Shugaban kasar Nijeriya za a ga cangi mai amfani.

Yahaya Bello a matsayinsa na Gwamnan jihar Kogi ya hada kan al’umman jihar suna zaune lafiya da juna , babu rigimar kabilanci ko tsakanin Manoma da Makiyaya.

Ga kuma saukin rayuwa da hadin kan matasa da kaunar juna da bunkasa tattalin arziki.

Saboda haka idan muka zabe Yahaya Bello a matsayin Shugaban Nijeriya. Kasar zata samu cigaba zata samu zaman lafiya mai daurewa.

Taron da ya samu halartan Manyan yan Siyasa maza da mata  daga jihar Nasarawa. Ciki harda Tsohon Jakadan Nijeriya a kasashe nahiyar Turai. Alhaji Musa Ilu Muhammad, wanda shima ya tofa albarkacin bakinshi. Hajiya Asabe Okode da Tsohon kakakin Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar Lafia da da sauran manyan baki duk sun tofa albarkacin bakinsu.

Bayan kammala taron an bude ofishin bakin suka zaga ofis ofis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *