BA MAMAYA MAKEYI A UKRAINE BA – HUKUMAR RASHA

baya bayan nan hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasar Rasha ta haramtawa kafafen yada labarai masu zaman kansu kwatanta harin da Moscow ta kai kan Ukraine a matsayin “mamaya” ko kuma shelanta yaki”.

Yayin da sojojin Rasha suka shiga birnin Kyiv na Ukraine, ma’aikatar tsaron Moscow ta umarci kafafen yada labaran Rasha su tsaya kan bayar da alkaluman da suka faru a hukumance.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta zargi wasu kafafen yada labarai masu zaman kansu da yada bayanan da ba su da tabbas a cikin al’umma game da hare-haren da sojojin Rasha suka yi a garuruwan Ukraine da kuma kashe fararen hula

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *