DA KAMAR WUYA – Najeriya ta shiga cikin sahun jerin kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha

Najeriya ta shiga cikin sahun jerin kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha

Majalisar dinkin duniya ta gudanar da zaben gaggawa kan yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine Kasashe biyar kacal cikin kasashe 193 suka goyi bayan Rasha yayinda kasashe 35 suka ce babu ruwansu.

Najeriya na cikin jerin kasashe 141 da suka yi Alla-wadai da abinda Rasha ke yi

Najeriya na cikin jerin kasashen duniya 141 da suka kada kuri’a ranar Laraba a majalisar dinkin duniya don a hukunta Rasha bisa hare-haren da take kaiwa kasar Ukraine.

Hakazalika kasashen sun bukaci Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine kai tsaye.

Wannan zabe da aka kada ranar Laraba na nufin hukunta Rasha.

Cikin kasashe 193 da suka halarci zaman taron ganganmin majalisar tsaron, mutum 141 su zabi a hukunta Rasha.

Rabon da a gudanar da taron gangami na gaggawa irin wannan tun shekarar 1982, a cewar UN a shafinta na yanar gizo.

Kasashe 35 sun janye daga zabe inda suka ce ba zasu ce hukunta Rasha ba kuma ba zasu ce kada a hukunta Rasha ba.

Kasashen sun hada da kasar Sin, Afrika ta Kudu, Mali, Madagascar, dss.

Kasashe 5 kuwa sun goyi bayan Rasha. Sun hada da Syriya, Belarus, Koriya, Eriteriya da Rashan da kanta.

Jakadar Amurka na majalisar dinkin duniya, Linda Thomas ta bayyana alfaharinta bisa sakamakon wannan zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *