AFCON 2023: Za a raba jadawalin shiga gasar kofin Afirka ranar Talata

AFCON 2023: Za a raba jadawalin shiga gasar kofin Afirka ranar Talata

Daga Musa Gwale

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf za ta yi bikin raba jadawalin neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2023.

Code d’Ivore ce za ta karbi bakuncin wasannin da za a yi a 2023, bayan da Kamaru ta gudanar da gasar 2020, wadda aka yi a 2022.

Hakan ya biyo bayan cutar korona da ta kawo tsaiko, sannan aka yi gasar tsakanin Janairu zuwa Fabrairun 2022.

Za a raba jadawalin ne a Afirka ta Kudu ranar Talata, inda Thomas Mlambo zai gabatar tare da Solomon Kalou da kuma Lucas Radebe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *