KO KUNSAN – Erik ten Hag ya zama sabon kociyan Manchester United

Erik ten Hag ya zama sabon kociyan Manchester United

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta nada Erik ten Hag a matsayin sabon kociyan ta wanda zai maye gurbin Ralf Rangnick da yake koyar da kungiyar a matsayin rikon kwarya.

Kociyan, Mai shekara 52, dan asalin kasar Holland, ya amince da kwantaragin shekara uku, amma yana da zabin tsawaita kwangilarsa da shekara daya.

Mai koyarwa Rangnick, wanda ya zama kocin rikon kwarya a kungiyar tun bayan korar Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamban shekarar data gabata, zai koma matsayin mai bayar da shawara a kungiyar.

Tuni dai wasu rahotanni suka bayyana cewa ‘yan wasa da dama zasu bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *