Gwamna Abdullah Sule yaga chanchantar Matawalle a matsayin Sanata gaba da gaba – Yusuf Loko

Gwamna Abdullah Sule yaga chanchantar Matawalle a matsayin Sanata gaba da gaba
– Yusuf Loko

Daga Zubairu Lawal

Gwamna Abdullah Sule yaga chanchantar Matawallen Toto a matsayin Sanata.

Gwamna Abdullah Sule yaga dubban jama’a da suka nuna kauna da goyon baya ga Barrister Labaran Shuaibu Magaji gaba da gaba a gidan Gwamnati.

Chanchantar Labaran Magaji ya sanya dubban jama’a sukayi kiranshi da ya fito Takarar.

kungiyoyin jama’a maza da mata a yankin mazaber Nasarawa ta yamma a kullun suna nuna kauna ga Barrister Shuaibu Labaran Magaji.

Alherin da matawallen Toto yakeyiwa jama’an yankin Nasarawa ta yamma da sauransu ya sanya suke nuna kauna gareshi.

Mutani da Kansu suka gayyace Labaran Magaji ya zo yayi Takarar Sanata a wannan mazaber.

Ganin yadda kungiyoyin jama’a daga Toto Nasarawa keffi Garaku Karu suka rinka kiran matawallen Toto saboda yayi masu Takarar Sanata shi ya sanya Matawalle ya amsa kiransu.

Matawalle a amsa kiran al’umman yankin Nasarawa ta yamma a gaban Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule a ranar da ya kai masa ziyara.

“Duk abinda akace al’umma sun nuna kauna a gareka to ya kamata a matsayin ka na mutumin kirki sai ka amsa kiran jama’a.”

Ganin chanchanta da Sanin ya kamata da alherin da matawalle keyiwa jama’a.

Yasa a kullun suna tare da shi shima yana tare da su. Hakan ya sa Gwamna Abdullah Sule ya yabama Tafiyar Matawalle ya kuma samata albarka. Inji Daraktan yakin niman zaben Dan Takarar Sanata a shiyar Nasarawa ta yamma .
Alhaji Yusuf Loko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *