Matawallen Toto yafi kowa Chanchanta a yan takarar Sanata – Inji Alhasan Gambo Chocho

Matawallen Toto yafi kowa Chanchanta a yan takarar Sanata Inji Alhasan Gambo Chocho

Daga Zubairu M Lawal

Matashin Dan siyasa cikin tawagar matasan yankin Nasarawa ta yamma Alhasan Gambo Chocho ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Lafia.

“Sunana Alhassan Gambo Chocho Dan asalin garin Toto ina kada kuri’a a Akwatin gidin tsada dake cikin birnin Toto”

“Abinda yasa nace Barrister Labaran Magaji Matawallen Toto shi yafi chanchanta Jam’iyyar APC ta bashi tiketin yin takarar Sanata a mazaber Nasarawa ta yamma
Saboda adalci da sanin ya kamata”.

Idan mukayi la’akari da tsarin siyasan yankin Nasarawa ta yamma dukanmu uwa dayane uba dayane.
Duk wadanda suka tabayin Sanata a wannan yankin ta yammacin Jihar Nasarawa yanzu Allah ya hadamu guri daya a gida daya, duk muna APC.
Sanata Abubakar Sodangi daga Karamar Hukumar Nasarawa yayi shekara 12 Dan APC ne.

Sanata Abdullah Adamu yayi shekara 12 Dan APC ne , yanzu shine uban duk wani Dan APC dake Nijeriya.

Kaga kenan munzama uwa daya uba daya.

Sai mu duba adalci da yadda ya chanchanta tunda dukaninmu yan Jam’iyyar APC ne, chanchanta za a duba.

Inane basu taba rike kujerar Sanata a wannan yankin ba?.

Sai akai takarar Sanata wannan bangaren. Kaga shine adalci da sanin ya kamata.

Duk da cewa mafiya yawan yan siyasan yankin Nasarawa ta yamma na Jam’iyyar APC sun amince ayi wannan tsarin, hakan yayi dai dai .

Kuma mu a Karamar hukumar Toto muna da tarin yan siyasa muna dunkulo kuri’a mai yawa lokacin zabe mu kada waje daya ga Dan takarar da mukeso.

Shi yasa yanzu mamyan yan siyasan Karamar hukumar Toto suka zauna sukayi shawara kan waya kamata ya wakilce wannan shiyar tunda dama tazo garemu?.

Aka duba akaga chanchantar Barrister Labaran Magaji, aka mikawa jigajigan yan siyasan Nasarawa ta yamma suma sukaga chanchantarshi, suka amince.

AlHasan Gambo Chocho yayi kira ga matasa dasuyi kokari suje mazabersu su yankan katin zabe saboda lokaci yayi da yanzu haka ana ridistan katin zabe soyayyan Dan takara bashi yuhuwa sai da katin zabe.

Ya qara da cewa Barrister Labaran Magaji mutumne mai tausayi yayi imanin zai kula da rayuwar al’umman wannan yankin fiye da tunanin mutum.

Gambo Chocho yace; yayi aiki da Matawallen Toto lokacin Ali Akwe Doma, “na shedeshi da sanin ya kamata da halin tausayi da kaunar jama’a. Saboda kyautarshin har ina kiranshi Mr. Atol – Atol.”

Kuma zai kara kaimi wajen jajircewa yaga an samar da abubuwan cigaba da matasa zasu amfana daga jihar ko tarayya.

Zai hada kai da Gwamna Abdullah Sule domin kara tabbatar da zaman lafiyar wannan yankin namu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *