Mutumcina shine na zabe Matawallen Toto a matsayin Sanata – inji Chairman Kokona

Mutumcina shine na zabe Matawallen Toto a matsayin Sanata – inji Chairman Kokona

Daga Zubairu Lawal

A yayin ziyarar tattaunawa tare da neman goyon bayan al’ummar ƙaramar hukumar Kokona dake jihar Nassarawa, ɗan takarar Kujerar Sanatan yammacin jihar Nassarawa, Barr. Labaran Magaji Matawallen Toto, tare da tawagar yaƙin neman zaɓen sa karkashin jagorancin Hon. Yusuf loko madugu uban tafiya.

Shugaban ƙaramar hukumar Kokona Hon. Auwalu Adamu, ya ce babu maganar ɓoye-ɓoye ranar zaɓen fidda gwani, kuri’a shi ta matawalle ce, sauran kansilona da da mataimaki na kowa yana da ikon zaben abin da ya ke so.

“Lamarina babu ƙarya ko yaudara a ciki, haka shine mutunci na gaskiya ɗaya ce kuma daga kin ta sai ɓata.”

Bayan ganawa da dukkanin Exco na ƙaramar hukumar, tawagar Matawallen Toto sun gana da Basaraken Gargajiya, Abaga Toni domin neman albarka da kuma girmamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *