ABIN TSUSAYI : Anyi Garkuwa da jaririya yar kwana biyar ana niman miliyon 100 a hannun talakawa

KO KUNSAN : Yadda Jaririyar da akayi garkuwa da ita ke rayuwar a hannu yan Bindiga a daji?

Daga Amina Sa’idu

Yau kwana 35 wannan jaririyar tana hannun masu garkuwa da mutane
Ita yaririyar dai an haifeta  da kwana 5 ne sai masu garkuwa da mutane suka shiga har cikin gida suka dauketa a hannun mahaifiyar ta wani daga cikin masu garkuwa da mutanen sai tausayi ya kamashi yace gaskiya a hada har da uwarta inda nan take suka tasa keyar uwar jaririyar tana cikin jego kwana 5 da haihuwa haka suka tasa kiyar ta suka nufi daji da ita bayan sun hada mutane 5 a cikin gidan

Wata majiya tace masu garkuwa da mutanen sun kira dangin mai jegon bayan yan kwanaki da cewa suna neman Naira Milyan 100 kafin su sako jaririn da Uwar jaririn.

Bisa hakane waliliyarmu tayi takakkiya ta ziyarci dangin mai jegon don jin masu jaje tare da jin ko wani hali ake ciki zuwa yanzu kwanaki 35.

Tuni sukace har yanzu ba labarin sako wannan jaririyar da sauran wadanda akayi garkuwan dasu.

Don haka suke rokon al’umma dasu taimaka masu da addu’o’i kuma sun roki  gwamnati ta taimaka masu kamar yadda aka taimakawa wasu da irin wannan jarabawar ta affaka masu.

Bincike ya tabbatar da cewa maharan sun kwashe a kalla mutane 6 ne a gida daya duk da jaririyar.

Wannan lamarin ya farune a wata anguwa da ake kira Sabuwar Abuja dake a garin Giwa a jihar kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *