KO KU KARANTA ; Yadda Rikicin cikin gida ya hana Jam’iyyar APC mai mulki gudanar da zaben a Nasarawa

KO KUNSAN ; Rikicin cikin gida ya hana Jam’iyyar APC mai mulki gudanar da zaben a Nasarawa

Rikicin cikin gida ya hana Jam’iyyar APC mai mulki gudanar da zaben fidda gwani na Majalisar Dokokin jihar a wasu Kananan Hukumomi guda takwas 8 a fadin jihar dake da kananan Hukumomi 13

Majalisar Dokokin jihar Nasarawa tanada membobi 24 ne daga Kananan Hukumomi 13.

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa reshen jihar Nasarawa Sanata John Mammam ya shedawa manema Labarai cikin Daren ranar alhamis 26/5/2022.
Cewa zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC ya gagara gudana cikin wasu Kananan Hukumomi 8 a fadin jihar sakamakon rikicin cikin gida na masu gudanar da zaben fidda gwani.

Yace; rigingimun sun sanya dakatar da zaben bisa ummurnin Shugaban jam’iyyar ta kasa, injin John Mammam.
Ya zuwa yanzu dai Jam’iyyar bata sanar da ranar da zata maimaita zaben fidda gwanin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *