Ina kira ga Jami’an tsaro su Saki mutani na da suka kama – Matawallen Toto

Ina kira ga Jami’an tsaro su Saki mutani na da suka kama – Matawallen Toto

Barrister Labaran Shuaibu Magaji (Matawallen Toto yayi kira ga Jami’an tsaro dasu saki matasan da suka kama.

Magaji yace; a jiya Lahadi anyi amfani da Jami’an tsaro fiye da 100 saboda kokarin hanawa ko magudin murde zabe.

Yace; Malamin zaben anyi amfani dashi da kuma Jami’an tsaro ta yadda ake son amfani da masu zabe na boge.

Matasa da jigogin yan siyasa dake yankin Keffi ta yamma sunki amincewa suna bukatane ayi zaben gaskiya.

Barrister Magaji yace; bai kamata Jami’an tsaro su kama masa mutani ba.

Saboda mutanin nan babu makami a hannunsu kuma basu taba kowa ba. Iyaka sunce basu bukatar ayi masu magudi, suna bukatar abarsu su zabe Wanda suke so.

Barrister Labaran Shuaibu Magaji yayi kira ga Jam’iyyar APC ta sanya baki a sake mutaninsa kuma a gudanar da zaben fidda gwani na gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *