KO KARANTA – Matsayin Tunubo a siyasan 2023

“Ni fa ina son Obasanjo saboda da wuya ka samu shugaban da yasan Nijeriya da ƴan Nijeriya kamar Baba Aremu. Idan kana son saninsa samu lokaci ka karanta littafan daya rubuta.

Na ƙara yarda da yadda Obasanjo ya san ƴan Nijeriya da na ji Bola Ahmed Tinubu ya ce iƙirarin da cewa shekarunsa na haihuwa 69. A lokacin da ƴarsa ta fari Folashade ta cika shekaru 61. Shin Tinubu yana shekara takwas ya haifeta kenan?

Obasanjo a littafinsa ya bayyana Tinubu a matsayin tantirin maƙaryaci har yake cewa komai na Tinubu ƙarya ne idan ban da Tinubun shi kansa. Lokacin yana Gwamnan Legas ba na mantawa Marigayi Cif Gani Fawehinmi ya kai shi ƙara kotu yana tuhumarsa da takardun boge.

Yanzu ga shi ya faɗi shekarun bogi, wani yake cewa hatta dalar da yake raba wa ta bogi ce. Shakka babu kun san duk abin da zai faɗa a yaƙin neman zaɓe boge ne. Sai dai idan ba a yi hankali ba a ranar zaɓe zai iya zuwa da ƙuri’a boge. Tabbas idan ya ci kuwa ba mai hana shi mulkin boge.

Daga Taskar Haruna Uba .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *