KO KUNGA : Yadda duban jama’a suka tarbi Matawallen Toto a Nasarawa ?

KO KUNGA : Yadda duban jama’a suka tarbi Matawallen Toto a Nasarawa ?

Daga Zubairu Lawal

Dubban mutani maza da mata sun tarbi Dan takarar Sanata na jam’iyyar APC a mazabar Nasarawa ta yamma Hon.Barista Shuaibu Labaran Matawallen Toto.

A yau Asabar 18/6/2022, Duban magoya bayan da suka fito daga yan kin mazabar Nasarawa ta yamma sunyi jerin gwanon motoci da Babura a Karamar Hukumar Abaji dake yankin Abuja, domin tarban masoyin nasu.

Tun misalin karfe 9am motocin daga Keffi, Karu, Kokona, Nasarawa dama Toto makare da jama’a suka fara cicirindo a garin Abajin.

Misalin 12pm Matawalle ya iso inda ya tarar da dubban jama’a suna sauraron isowarsa.

An gudanar da jerin gwanin Motocin daga Abaji zuwa Toto.

Ta wagar ta yada zango a fadar Sarkin Toto Ohiniyi Ona Muhammad Azaki inda suka mika gaisuwa Sarkin ya sanyawa tawagar albarka.

Ya kuma bukaci a gudanar da harkan siyasa cikin kwanciyar hankali.

Tawagar ta wuce zuwa filin taro a makarantar Primary dake tsakiyar garin Toto.

Mutani da dama sun gudanar da jawabi daga sassa dabam dabam.

Masu jawabi sunyi kira ga Shugabannin Jam’iyyar APC reshen jihar Nasarawa da subi ummurnin kwamitin sauraron koken zabe da tace, a maidawa Barista Labaran Magaji nasarar shi na zaben fidda gwani, sakamakon ta gani magudin da akayi yadda akayi amfani da masu zaben boge aka sauya sunayen na gaskiyan a karamar hukumar Nasarawa da Keffi.

Masu jawabin sun nuna jajircewa da Matawallen yayi wajen ganin an gudanar da zaben fidda gwani cikin gaskiya a matsayin matakin nasara.

Sun kuma bukaci Matawallen ya dauki duk matakin shari’a , har sai an tabbatar da sunanshi cikin jerin yan takarar da zasu gudanar da babban zabe a 2023.

Shugabannin jam’iyyar APC na Kananan Hukumomin Keffi Karu, Kokona, Nasarawa da Toto harma da wasu daga jihar suka hakarci taron suka gudanar da jawabin goyon baya da fatan Allah ya sanya a maidowa Matawallen nasarar shi domin Jam’iyyar APC ta kai ga nasara a zaben 2023 a wannan yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *