KO KUNSAN -/ Kungiyar Arsenal Ta Kammala Sayan Vieira Daga Porto

KO KUNSAN -/ Kungiyar Arsenal Ta Kammala Sayan Vieira Daga Porto

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala Sayan dan wasan tsakiya na kungiyar FC Porto, Fabio Vieira, akan kudi fam miliyan 34.

Tun a satin daya gabata ne dai kungiyoyin biyu suka cimma matsaya bayan doguwar tattauna wa a tsakanin su.

Vieira yana daya daga cikin ‘yan wasan da kociyan kungiyar, Mikel Arteta ya bukaci kungiyar ta siyo masa domin bunkasa tawagar a kakar wasa mai zuwa.

Bayan kammala Sayan Vieira, yanzu hankalin Arsenal zai karkata ga neman dan wasan Manchester City, Gabriel Jesus, wanda ake saran nan gaba kadan za’a shiga tattauna wa tsakanin kungiyoyin biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *