KO KUNSAN – Ya buga wasa 169 yaci kwallaye 120 kafin yayi hijira zuwa Bayern Munich

Ya buga wasa 169 yaci kwallaye 120 kafin yayi hijira zuwa Bayern Munich

Daga wakilinmu

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta tabbatar da cewa dan wasa Sadio Mane ya kammala komawa Bayern Munich kan kudi fam miliyan 35 kan yarjejeniyar kakar wasa uku.

A cikin yarjejeniyar, Liverpool za’a bawa Liverpool zunzurun kudi fam miliyan 27.4 da karin fam miliyan shida kan yawan buga wasa da wasu fam miliyan uku kan kokarin dan wasan da nasarorin da Bayern Munich za ta yi.

Mane, Mai shekara 30 a duniya Kuma dan kasar Senegal ya koma Liverpool ne akan kudi fam miliyan 34 daga Southampton a shekarar ta 2016.

Ya buga wasanni 269 a Liverpool inda ya zura kwallaye 120 sannan ya taimaka aka zura guda 48.

A shekaru shida da yayi a Liverpool, ya lashe gasar firimiyar Ingila da kofin zakarun turai na Champions league da FIFA Club World Cup da Eufa Super Cup da kofin kalubale na FA da kuma gasar Carabao Cup.

A farkon wannan shekarar ne dai ya taimaka wa kasar sa ta Senegal ta lashe kofin Nahiyar Afirka da kasar Kamaru ta karbi bakunci.

Ya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *