KU KARANTA – Tinubu bashi da takardan kammala karatun Sakondire
Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya fada wa hukumar zabe INEC cewa wasu da bai san ko su wanene ba sun sace takardun karatunsa Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin cike fom na takarar shugaban kasa wacce ya mika wa INEC gabanin zaben 2023 inda aka kawai karatunsa na Jami’ar Chicago ya saka babu frimare da sakandare Sai dai, bisa alamu wannan bayanin da Tinubu ya rubuta a takardar zaben na 2023 ya sha banban da abin da ya fada wa INEC yayin zaben 1999 inda ya ambaci sunan makarantun da ya yi frimare da sakandare
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya shaidawa hukumar zabe mai zaman kanta cewa wasu mutane da bai sani ba suka sace masa takardun karatunsa lokacin ya yi hijirar dole zuwa kasar waje, Daily Trust ta rahoto.
Jam’iyya Zata Maka Tinubu a Kotu Kan Bayanan Bogi a Takardun Karatunsa
Tsohon gwamnan na Jihar Legas, ya bayyana hakan cikin takardan rantsuwa da ya gabatarwa INEC yayin cike fom din takarar shugaban kasa cewa ya ‘tafi hijirar dole daga Octoban 1994 zuwa Octoban 1999 kuma da na dawo sai na gano wasu da ban sani ba sun sace kayayaki na har da takardan shaidan karatu da ake nema a sakin layi na 3.’
A yayin da Tinubu ya tsallake bayanai na karatunsa na sakandare da frimare yayin cike fom din na INEC, ya ce ya yi karatu a Jami’ar Chicago tsakanin 1972 da 1976 inda ya yi digiri a bangaren Nazarin Tattalin Arzikin.
Ya kuma ce yana da digiri a bangaren Kasuwanci da Gudanar da Mulki da kuma satifiket na aiki a matsayin Akanta.
Wasikar ta Tinubu, bisa alamu ta ci karo da bayanan da ya bayar a zaben da suka gabata a 1999, a lokacin da ya yi takara kuma ya ci zaben gwamnan Jihas Legas.
A lokacin, ya yi ikirarin ya yi karatun frimare a St Paul Children’s Home School,Ibadan, daga 1958 zuwa 1964; yayin da ya yi karatun sakandare a Government College Ibadan (GCI), daga 1965 zuwa 1968.
Ya yi ikirarin daga Ibadan ya kuma tafi Richard Daley College, Chicago, daga 1969 zuwa 1971.
Sai dai, fitaccen lauyan Najeriya marigayi Gani Fawehinmi ya kallubalance takardun karatun yana mai cewa na bogi ne.
An yi shari’a da Fawehinmi har zuwa kotun koli, inda aka yi watsi da karar saboda kuskure na tsarin shigar da kara amma ba don rashin hujja ba.