RANAR CIWON HANTA TA DUNIYA:Ma’aikatan kiwon Lafiya ta Nasarawa Ta Wayar Da Kan Al’umma.

RANAR CIWON HANTA TA DUNIYA:Ma’aikatan kiwon Lafiya ta Nasarawa Ta Wayar Da Kan Al’umma.

Daga Zubairu Lawal

Ma’aikatan kiwon lafiya ta jihar Nasarawa na farin ciki gayyatar al’umma don tunawa da Ranar Cutar Hanta ta Duniya ta 2022 wato ‘World Hepatitis Day 2022 Pop-Up’.

Wannan bayanin ya fito ne a wata sanarwa da Cibiyar lafiya ta kasa reshen jihar Nasarawa ta fitar a ranar Alhamis, inda ta bukaci da suyi gaggawan zuwa ayi masu gwajin cutar hanta.

Kwamishinan kiwon lafiya ta jihar Dr.Ahmad Baba Yaya ya sanar da haka sa’ilin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Kwamishinan ya gargadi al’umman jihar dasu daina ta a mali da gurare mara tsafta,  domin ana iya kamuwa da cututtuka harma dana Hanta a gurare Mara tsafta.

.yace; cutar hanta ta kasu kashi biyar harafin A,B,C,D,E.

Yace; cikin cutar akwai wanda ake iyayi masa rigakafi, akwai kuma wanda ba ayi masa riga kafi idan an kamu dashi saidai ayita shan Magani.

Sannan akwai Wanda ake warkewa idan ansha msgani akwai kuma Wanda baya warkewa saidai cutan ba zaiyi tashiri a jikin mutumba idan ana shan magani.

Ya qara da cawa an iya daukar cutan ta hanyoyin gamayyan haduwan jini.

Amma ba a iya daukar cutan ta hanyoyin runguman juna ko ta hanyan zufa kamar yadda wasu ke cewa.

Sai dai jariri yakan iya daukar cutan a cikin mahaifiyarshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *