Sabon Rikici Gwamnonin APC Sun Ki Amince Wa Elrufa’i Ya Jagoranci Kamfen Din Tinubu?

Sabon Rikici Gwamnonin  APC Sun Ki Amince Wa Elrufa’i Ya Jagoranci Kamfen Din Tinubu?

Ba da jimawa ba Gwamnanonin jam’iyyar APC suka kammala wani taro, inda suka yanke shawarar kin yarda da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru Ahmad Elrufa’i a matsayin wanda zai jagoranci yakin neman zaben shugaban kasa na Bola Ahmad Tinubu.

 

A wajen taron, gwamnoni sun amince Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong da tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adamas Oshiomhole ne za su jagoranci yakin neman zaben Tinubu da Kashim Shettima domin kai wa ga kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

 

Idan dai har hakan ta tabbata, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru Elrufa’i zai tashi ba shi ga tsuntsu, ba shi ga tarko a wannan tafiyar, kamar yadda masu nazari harkokin siyasa suka bayyana. 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *