Shari’an Zaben kujerar Sanata a Mazaber Shugaban APC ta Kasa na daukar zafi

Shari’an Zaben kujerar Sanata a Mazaber Shugaban APC ta Kasa na daukar zafi

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Shari’an zaven kujerar Dan Majalisan Dattijai a Mazaber Shugaban jam’iyyar APC ta kasa tana kara zafi.

Shari’an wanda Barrister Labaran Shuaibu Magaji ya shigar yana kalubalantar nasarar Arc.Shehu Tukur kan zaben fidda gwani da ya gudana a ranar 4/6/2022 wanda yace tana cike da almundahana.

Tuni dai Alkalin Kotun Gwamnatin tarayya dake zamanta a Lafia. mai shari’a Nehizina Idumudia Afolabi ta fara saurarun karar tun a watan jiya.

A ranar Laraba 3/8/2022 Lauyoyi sun cigaba da tada jijiyoyin wuya da musayan kalamai domin kare wadanda suke wakilta.

Sai dai abubuwan da ya daurewa mai shari’an kai a zaman da akayi ranar Laraba yayin da Layoyin Labaran magaji suke kalubakantar nasarar Shehu Tukur a matsayin an sauyo sunayen masu zaben yan takara a Karamar Hukumar Keffi da Nasarawa.

Sukace takardan da asalin sunayen masu zaben na asali yake an sauya, anyi amfani da wani takardan da sunaye na dabam.

Mai shari’an Nehizina Idumudia Afolabi ta bukaci azo da wakilin Hukumar zabe ( INEC) da ya gudanar da zaben fidda gwani a ranar.

Sakamakon takardan dake dauke da bayanan masu zaben akwai sabanin sanya hannaye dabam dabam.

Tuni ta bukaci da Mr Omale Samuel ya kawo kansa gaban Shari’a a ranar 31/8/2022 domin bambamce asalin sanya hannunsa cikin takardun.

A nasa jawabin Barrister Labaran Shuaibu Magaji yace yana da tabbacin zaiyi nasara a wannan shari’ar. Domin gaskiya zatayi halinta.

Ya kara jaddada cewa yana tara da Jam’iyyar APC yana tara da Gwamna Abdullah Sule.

A nasa jawabin Barrister Gali Umar Ahmed yace; muna da hujojin da zasu tabbatar mana da nasara cikin wannan shari’ar.

Yanzu gashi Kotu ta fara gayyatar mutanin da suka sauya al’amuran dasuzo su kare kansu.

Yace; muna da hujoji da sunayen masu zaben Dan takara na asali da jebun da akayi amfani dasu.

Zuwan Mr Omale Samuel zai kara tabbatar da gaskiyar maganar da mukeyi, na cewa anyi amfani da sunayen mutanin da babu sunansu a cikin masu zaben.

Barrister Gali yace,; muna jiransu muhadu ranar.

Shima Barrister Ibrahim Bawa mai kare jam’iyyar APC yace; Kotu ta bukaci Ma’aikacin Hukumar zaben Mr.Omale Samuel da ya gurfana gabanta saboda bam bamci sanya hannaye a kan takardun zaben.

Yace; shari’a macece mai ciki ba asan mai zata haifa ba. Amma yana fatan a gudanar da shari’ar lafiya a gama lafiya.

Shina Lauyan wanda ake karar yace suna da cikaken hujojin da zasu gabatarma kotu cewa sunyi nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *