Cacar Bakin Wike Da Sanata Makarfi

Cacar Bakin Wike Da Sanata Makarfi

Cacar baki ta kaure tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike game da rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP.
An ruwaito Sanata Makarfi a cikin shirin talabijin na Channels a yau Talata yana bai wa Wike shawara kan cewa fushi ba nasa ba ne, kuma yanke shawara a cikin fushi ba ya haifar da ɗa mai ido.

Don haka ya ce yana kira ga Wike da Peter Obi da Sanata Rabi’u Kwankwaso su zo su haɗa hannu da Atiku don PDP ta karɓe mulki a hannun APC a zaɓen 2023 da ke tafe.Sai dai a martaninsa a wani taron ƙaddamar da ayyuka a Jihar Ribas, Gwamna Wike ya ce wa Makarfi ya fara da gida tukuna kafin ya tsallaka waje ya ce zai ba wani shawara.

A cewar Wike, Makarfi ka fara da gida, ka tabbatar da PDP ta karɓe Jihar Kaduna daga APC tukuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *