Shari’an zabe Sanata Lauyoyi (SAN) sama da 10 suna goyon bayan Matawalle a Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
Manayan Lauyoyi masu mukamin SAN sama da goma sun ziyarci Babban Kotun Gwamnatin Tayarra dake Lafiya domin taimakawa Dan uwansu Barrister Shu’aibu Labaran Magaji wanda yake karar nasarar Arc.Shehu Tukur a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a mazaber Nasarawa ta yamma.
Da yake zantawa da manema labarai Shugaban tawagar Lauyoyin da suka zo taimakawa Labaran Magaji kimanin su 10 masu mukamin SAN,
Barrister Johnson Jacob yace tawagarmu ta manyan Lauyoyi munzone domin taimakawa Labaran Magaji bisa kokarinsa na niman hakinsa.
Yace; Shari’a ce, kuma hanyar da Labaran Magaji ya dauka itace kadai hanyar gaskiya domin idan aka zalunce mutum yana da hakin zuwa kotu.
Ya kara da cewa zamu cigaba da kokarinmu har sai munyi nasara.
Dan takarar kujerar sanata a jam’iyyar APC a mazaber Nasarawa ta yamma Barrister Shu’aibu Labaran Magaji yace yananan daram a jam’iyyar APC sai ya karbi hakinsa.
Magaji yace; mu masu biyyayane kuma masu kishin jam’iyyar APC muna tare da jam’iyyar APC daga sama har kasa. Muna tare da Gwamna Abdullahi Sule.
Barrister Magaji ya bayyana hakane bayan daga karar da ya shigar yana kalubalantar nasarar Acr Shehu Tukur a zaben Fidda gwani da ya gabata.
Shari’ar da aka sanya za a zauna a ranar Laraba 31 ga watan takwas. Mai shari’a Nehizina Afolabi daga Kotun Gwamnatin Tarayya dake Lafia bata samu zuwa ba.
maga takardan Kotu ya sanar da daga sauraron shari’ar zuwa 7/9/2022.
Barrister Mubaraq mai kare Shehu Tukar yace; rashin zuwan Alkali katu ba sabon abubane yana faru ya danganta da yanayi.