Kabilar TV suna tare da Gwamnatin Abdullahi Sule a 2023

  1. Kabilar TV suna tare da Gwamnatin Abdullahi Sule a 2023

Inji Kwamared Pite Ahemba
Shugaban Kungiyar kabilar T.V mazauna jihar Nasarawa Kwamared Piite Ahemba yace Mambobin kungiyar TV masu yawan gaske suna nuna goyon bayansu ga Gwamna Abdullahi Sule.
Shugaban kungiyar ya bayyana haka na a lokacin da tawagar yan kabilar TV mazauna Nasarawa suka kai ziyarar goyon baya ga Gwmna Injiniya Abdullahi Sule a gidan Gwamnatin a ranar alhamis.
Kwamared Pite Ahemba yace; al’umman TV mutanine masu bukatar zaman lafiya a duk India suke zaune.
Kuma mutanine masu biyayya, saboda haka suna tare da wannan Gwamnatin dari bisa dari.
Gwamna Abdullahi Sule ya jinjinawa al’umman TV da suke zaune a jihar Nasarawa saboda yadda suka dauki muradin zaman lafiya a fadin jihar Nasarawa.
Gwamanan ya kara da cewa Gwamnatinsa tana da kyakyawar kudduri na tabbatar da zaman lafiya ga dukkan kabilun dake zaune a fadin jihar baki daya.
Gwamnan yace; babu abinda yafi zaman lafiya dade. Yayi kira ga al’umman TV da mafi yawansu  manomane dasu kara
tabbatar da zaman lafiya da abokan zamansu a duk yankunan da suke tare.
Gwamana ya baiwa kungiyar Mota da zasu rika gudanar da harkokin kungiyar tasu.
Itama kungiyar ta baiwa Gwamnan Sarautan gargajiya ta kabilar TV, mai taken (Zege Mule-U-Tiv)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *