INDA RANKA – Karfin hali Barawo a gidan yan Bindiga

INDA RANKA – Karfin hali Barawo a gidan yan Bindiga
Karfin hali sata a gidan yan’ bindiga: Masu garkuwa sun kama barawo dake yi masu sace-sace a gidajensu
Daga Taskar Labari
Wasu gungun yan bindiga a kauyen Kilili na jihar Katsina sun kama wani matashi da suka ce barawo ne dake zuwa gidajen su yana yi masu barna yana sace karafuna da sauran kayayyaki a gidajensu,
A wani bidiyo da Taskar Labarai  ta kalla an ga yadda yan bindgar suka daure matashin mai suna Halliru wanda ya ce shi dan kauyen Ranka ne, sannan suka gabatar dashi ga yan jarida kafin daga bisani suka mika shi ga hukumar soji domin a dauki mataki akansa.
Alh Usman Kachalla Rugga shine shugaban yan bndigar wanda ya shaidawa dan Jarida Usman Saleh Jino cewa dama sun dade suna neman kama masu zuwa suna yi masu sace-sace a gidajensu sai gashi yau Allah ya basu sa’a sun kama barawon,
Ya ce sunyi niyyar kashe shi to amma suka yanke shawarar gayyatar yan jarida cikin dajin domin nunawa Gwamnati irin kokarin da suke yi wajen kama baatagari, “kuma yanzu zamu baku shi a kaishi wajen hukuma su hukunta shi”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *