INEC ta nisanta kanta daga magudin zaben takarar Sanata a Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
Kotun Gwamnatin tarayya dake sauraron Shari’ar zaben fidda gwani a garin Lafia jihar Nasarawa karkashin jagorancin mai shari’a Afolabi Nehizena, ta cigaba da zamanta a jiya Laraba.
Mai shari’a Afolabi Nehizena, ta saurare Sheda na farko Mr, Omale Samuel ma’aikacin hukumar zabe ta kasa.
Tunda farko Barrister Shu’aibu Labaran Magaji yana kalubalantar nasarar Arc, Shehu Tukur bisa gudanar da zaben cike da almundahana.
A karar da Barrister Labaran Magaji ya shigar gaban Shari’a yana zargin an sauya sunayen masu zabe a mazaber Nasarawa da Keffi.
Yace; takardn da aka kawo mai dauke da sunayen mutanin dake Kananan hukumomin biyu kimanin mutum 125 bana gaskiya bane, an sauya sunayen asalin masu zaben. Sannan takardan ba asalin Wanda jami’in hukumar zabe Mr. Omale Samuel ya rubuta kuma ya sanyawa hannu bane.
Kan hakane Mai shari’a Afolabi Nehizena, ta bukaci Ma’aikacin hukumar zabe Mr Omale Samuel ya gurfana gabanta a ranar Laraba 7/9/2022.
Mr. Omale Samuel ya gurfana gaban Shari’a a madadin Wanda ya sanya hannu a lokacin zaben masu zaben yan Takara a yankin Nasarawa ta yamma.
Kotu ta mika masa takardu guda biyu masu dauke da sunaye mabambamta da hatimi mai kusan kamannin daya, amma akwai bambamci.
Mr. Omale Samuel ya nuna takardan da ya rubuta na asali kuma ya nuna hatimin da yake rattabawa bayan kammala rubut kan takardan.
Ya kuma nisanta kansa daga wancan da aka kwakwayo akayi amfani da sunansa sannan akwai sabanin kwanan wata inda a nashi takardan 15 ne ga wata a jebun takardan 10 ga wata.
Kotu ta tambaye Mr. Omale Samuel ko zaiyi sake maimatai hatiminsa da sanya hannu gaban Shari’a?.
Mr. Omale Samuel ya maimaita tayi daidai da takardan dake na asalin sunayen masu zaben yan Takara.
Bayan tambayoyin da Lauyoyi sukayima Mr. Omale Samuel ya amsasu kotu ta ganu da hujjojinshi ta kuma sallameshi.
Kotu ta daga zaman kotun ta kuma ce su saurare ranar yanke hukunci a zama na gaba.