KO KUNSAN – Hangen rashin nasara ya sanya Dan takarar Sanata daukaka kara kafin yanke hukunci a Nasarawa

Hangen rashin nasara ya sanya Dan takarar Sanata daukaka kara kafin yanke hukunci a Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
Dan takarar kujerar Sanata a mazabar Nasarawa ta yamma Arc.Shehu Tukur ya daukaka kara zuwa Kotun daukaka kara dake  garin Makurdi a jihar Benue.
Arc. Shehu Tukur shine Dan takarar kujerar Sanata a mazabar Nasarawa ta yamma a Jam’iyyar APC.
Arc. Shehu Tukur yana fuskantar turjiya daga abokin takararsa da suka fafata a zaben fidda gwani cikin watan shida a Jami’ar jihar Nasarawa dake garin keffi.
Barrister Labaran Shuaibu Magaji yana kalubalantar nasarar Arc. Shehu Tukur saboda magudin sauya sunayen masu zabe, da kuma yin amfani da takardan boge da sanya hannu da sunan Ma’aikacin hukumar zabe na boge.
Kotun Gwamnatin Tarayya dake sauraron korafin zaben jihar Nasarawa a garin Lafia, a karkashin mai shari  Afolabi Nehizena ta gayyaci  Ma’aikacin hukumar zaben Mr Omale Samuel.
Mr. Omale Samuel ya bayyana gaban shari’a kuma ya nisanta kansa daga rubuta takardan sunayen masu zabe na boge, ya kuma tabbatarwa  kotu da sunayen asali da sanya hannu da hatimisa.
Hangen rashin yin nasara ya sanya tuni Wanda ake karar ya garzaya zuwa kotun daukaka kara kafin wannan kotun ta yankin hukunci.
Suna kira da a sauya mai shari’ar, kuma wannan shedar basu amince da bayyanarsa gaban shari’a ba.
Suna kira ga kotun daukaka kara data dakatar da wancan kotun da shedar da akayi amfani dashi.
Masu hasashe na ganin cewa Dan takarar ya daukaka kararne saboda ganin cewa bazasuyi nasara ba.
Ko kuma jan kafa a mahangar gudanar da shari’a a kan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *