Yahaya Bello ya cancanta a Mukamin Shugaban matasa na yakin zaben Tinubi – Matawallen Toto


Yahaya Bello ya cancanta a Mukamin Shugaban matasa na yakin zaben Tinubi – Matawallen Toto
Aswaju Bola Ahmad Tinubu yayi amfani da cancanta wajen janyo Gwamna Yahaya Bello a matsayin Jagoran matasa na yakin niman zabensa a shekarar 2023.
Barrister Shuaibu Labaran Magaji yace; Gwamna yahaya Bello jarumin mutumne da ya kware wajen iya tafiyar da matasa ta kowani bangare.
Matawalle yace; baiwa Yahaya Bello Mukamin Kodineto na yakin niman zaben Tinubu zai janyowa Dan takarar APC samun karuwan miliyoyin matasa a yankin Arewacin Nijeriya da kasa baki daya.
Barrister Labaran yace; Gwamna Yahaya Bello mutumne da yake hidima da matasa. Cikin Gwamnatinsa yayi ayyukan na gani na fada kuma matasa sun amfana da tafiyar Gwamna Yahaya Bello.
Gwamna Yahaya Bello ya kware wajen gina tafiyar matasa a fadin Nijeriya.
Dan Takarar Sanata a Jam’iyyar APC a yankin Nasarawa ta yamma, Barrister Magaji yace; yana da yakinin matsayin da aka baiwa Gwamna Yahaya Bello zai taimakawa Jam’iyyar APC, wajen samun nasara.
Magaji yace; a kalla Gwamna Yahaya Bello zai iya tara matasa sama da miliyon 50 a lokaci guda a fadin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *