Zamu bunkasa harkan Kannywood a Arewacin Nijeriya – Gwamnan Nasarawa

Zamu bunkasa harkan Kannywood a Arewa – Gwamnan Nasarawa

Daga Zubairu Lawal
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa yayi alkawarin bunkasa harkan kungiyar Fina Finai na Arewa, Kannywood.
Gwamna Abdullahi Sule yace matasan Arewa dake sana’ar harkan Fina Finai da wakoki nishadi a kungiyar  Kannywood matasane masu hazaka. Suna da bukatar a tallafamasu domin fadada sana’arsu.
Gwamnan ya bayyana hakane ranar Talata 20/9/2022 a gidan Gwamnati dake garin Lafia, a lokacin da tawagar Sakamakon chanji karkashin jagorancin Alhaji Abdul’amata ( Mai kwashewa ) ta kai masa ziyara.
Gwamna Abdullahi Sule ya jaddada jin dadinsa da wannan ziyarar. Yakuma jaddada kudurinsa na taimakawa matasa masu sana’ar harkan Fina Finai a jihar Nasarawa dama Arewacin Nijeriya.
Yace; ko masu sana’ar harkan Fina Finai na kasar Amurka basufi namu na gida da komai ba. Face sun samu goyon bayane yasa suka daukaka.
Ya qara da cewa taimakawa masana’antar Kannywood gina matasane gaba da baya.
Gwamna Sule ya tabbatarma tawagar sakamakon  chanji cewa jam’iyyar APC tana tare dasu saboda gudumawa mai yawa da tawagar ta baiwa APC da Gwamnatinta.
Gwamnan yayi shagube ga Hamisu Bireka cewa “Idan kuka dawo rantsar damu nima zan rera wakokin Bireka saboda iyalina ta koyar dani”
Tunda farko Shugaban tawagar sakamakon chanji Alhaji Abdul’amat (mai kwashewa) yayi godiya ga Gwamna Abdullahi Sule saboda lokacin da ya basu na wannan ziyarar.
Alhaji Abdul’amat ya bayyana yadda tawagar sakamakon chanji ta taka mahimmiyar rawa a zaben Shugaba Muhammad Buhari.
Yace; irin wannan rawar da kungiyar ta taka abaya zata cigaba da maimaitawa ga duk Gwamnonin APC.
Mai Kwashewa ya sanya wakar da tawagar ta sakamakon chanji ta Kannywood ta rera ga dukkan Gwamnonin APC, inda aka yaba da ayyukan Gwamnan Abdullahi Sule.
Shima a nasa jawabin Shugaban Tawagar ta jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Lawal Ibrahim, ya bayyana godiyansa da zuwar tawagar ta kasa.
Ya kuma shedawa Gwamnan cewa kungiyar a nan jihar Nasarawa tana da mambobi sama da 5000, kuma masu katin zabe.
Yace; kungiyar tana kara samun mabiya masu tarin yawa a kullun cikin fadin jihar.
 
Yace; kunigiyar zata yayata manufofin Gwamnan Abdullahi Sule a dukkanin kananan hukumomin jihar.
 
Daga karshe Alhaji Abdul’amat ya mikawa Gwamnan Abdullahi Sule jaddawalin tsare tsaren kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *