KU SAURARA – Gwamna Abdullahi Sule ya zabe Jam’iyyar,,,,,,,,

Gwamna Abdullahi Sule ya yaba da yadda zabe ke gudana a Nasarawa

Daga Zubairu Lawal

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa yace; yaji dadin yadda zabe ke gudana babu labarin hayaniya ko korafi a Jihar Nasarawa.

Gwamnan ya bayyana hakane lokacin da ya kada kuri’arsa a mazabersa dake 002 tashar mota dake garin Gudi a Karamar Hukumar Akwanga dake Jihar Nasarawa.

Gwamnan yace; al’umman Jihar Nasarawa sun da kyakyawar tsari da kaunar juna hakan ya sanya kowa yana gudanar da zabensa bisa son duk Wanda ya keso babu nuna kyama da zai kawo damuwa.

Gwamnan ya yabawa al’umman Jihar Nasarawa saboda suna gudanar da zabe lafiya babu labarin tashin hankali a ko ina cikin fadin jihar.

Gwamna Abdullahi Sule yayi fatan Allah yasa a kammala zaben lafiya kamar yadda aka gudanarwa yanzu.

Haka zalika Gwamna Abdullahi Sule ya zabe jam’iyyar APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *