Gwamna Abdullahi Sule ya lashe zaben jihar Nasarawa
Daga Zubairu Lawal
Shugaban Hukumar zabe da ya jagoranci gabatar da zaben jihar Nasarawa Farfesa Tanko Ishaya ya bayyana Gwamna Abdullahi Sule a matsayin Wanda ya samu kuri’u mafi rinjaye a zaben Gwamna da ya gudana a jihar Nasarawa.
Farfesan ya bayyana Dan takarar Jam’iyyar APC Injiniya Abdullahi Sule a matsayn Wanda ya laahe zabe da mafi rinjayen kuri’a kan abokan takararsa.
Dan Takarar Gwamna na jam’iyyar APC Injiniya Abdullahi Sule ya su kuri’a- 347,209.
Inda ya kada abokin karawarsa na jam’iyyar PDP Hon.David Ombugadu mai kuri’a
– 283,016.