Kakakin majalinsa Nasarawa yayi kira ga Gwamna Sule da ya tafi da kowa da kowa a Gwamnatinsa

Kakakin majalinsa Nasarawa yayi kira ga Gwamna Sule da ya tafi da kowa da kowa a Gwamnatinsa
Daga Zuabairu Lawal
Kakakin Majalisan Dokokin jihar Nasarawa Hon. Balarabe Abdullahi ya koma kujerarsa a karo na uku.
Hon. Balarabe Wanda yake wakiltar al’umman mazaber Umasha  da Ugya ya samu nasarar maimaita kujerarsa a karo na uku.
Da yake jawabin godiya bayan kammala zabe. Hon. Balarabe Abdullahi yayi godiya ga al’umman mazabersa da suka sake  bashi dama ya kara jagorantarsu.
Hon. Balarabe yace; ayyukan da yakeyi na alheri zai kara ninkawa domin cigaban al’umman mazabersa.
Ya kara da cewa zai rungume kowa da kowa domin tafiya tare da kuma ansan shawarwari masu amfani daga jama’an mazabersa.
Kakakin Majalisan yayi godiya da Allah da ya dawo da Gwamna Abdullahi Sule kan kujerar Gamma karo na biyu.
Hon. Balarabe yace; akwai alheri so sai a dawowan Gwamna Abdullahi Sule kujerar mulkin jihar Nasarawa. Ya kuma yi kira da Gwamna Abdullahi Sule daya kara kokari wajen samar da ayyukanyi ga matasa domin cigaban al’umman jihar Nasarawa.
Sanna yadda ya samar da zaman lafiya mai dorewa da hadin kan al’umman jihar ya kara kwazo domin zaman lafiya shine gaba da komai.
Daga karshe yayi kira ga zabeben Gwamnan jihar da ya tafi da kowa da kowa a Gwamnatinsa ya janyo sauran jam’iyyun domin a tafi tare saboda gina jihar Nasarawa a mataki na gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *