An bayyana Ferguson da Wenger cikin fitattun Premier League

An bayyana Ferguson da Wenger cikin fitattun Premier League

An bayyana Sir Alex Ferguson da Arsene Wenger cikin fitattu a Premier League.

Ferguson, tsohon kociyan Manchester United, mai shekara 81, shine kan gaba a yawan daukar kofi a Premier League mai 13 jimilla.

Wenger tsohon kociyan Arsenal ya dauki Premier uku a kaka 22 da ya ja ragamar Gunners.

Dan kasar Faransa ya ja ragamar Gunners ta yi wasa a kakar 2003/04 ba tare da an doke ta ba, sannan ta lashe Premier League.

Ferguson da Wenger sune na farko da aka sanar a jerin fitattun masu horarwa a Premier League.

Tun a 2021 aka fara sanar da fitattun babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan da aka bayyana David Beckham da Dennis Bergkamp da Eric Cantona da Thierry Henry da Roy Keane da Frank Lampard da Steven Gerrard da kuma Alan Shearer.

A bara aka kara da sunan Sergio Aguero da Didier Drogba da Vincent Kompany da Wayne Rooney da Peter Schmeichel da Paul Scholes da Patrick Vieira da kuma Ian Wright.

Ferguson, wanda ya horar da Manchester United daga 1986 zuwa 2013, ya lashe Premier League biyu a jere sau biyu, karo da ban.

”Martaba ce mai girma idan ka karbi kyautar da aka ga kwazonka,” kamar yadda ya fada. ”Wannan kyautar ba ta kashin kaina ce ba.

”An yi min kan aikin da na gudanar a Manchester United shekara da yawa, saboda haka ina alfahari da kungiyar da ma’aikatanta da ‘yan wasa.

”Aiki na ya hada na faranta ran magoya baya, tarihin United da abin da na yi tsammani sune suka dunga karamin kwarin gwiwa.”

Wenger, mai shekara 73 ya koma horar da tamaula a Premier League a matakin bako a 1996, sannan ya lashe kofin a kakar farko a Arsenal.

”Ina son a sanni a matakin mai kaunar Arsenal, wanda ke martaba kungiyar, wanda ya bar aiki don ta kara fadada, fiye da matakin da take kai,” in ji Wenger.

”A zabe ka tare da Sir Alex martaba ce mai girma a tare dani. Kamar dambe ne tsakani ‘yan wasa biyu, za ka yi dambe kamar mahaukaci, sannan kowa ya kama gabansa.

”Amma daga karshe, ana martaba juna, kuma babbar dama ce kasance tare da shi, inda muke tuna hamayyar da muka yi da juna a baya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *