KU SAURARA : Sanarwan sabuwar Gwamnatin Kano ya janyo cece kuce.

KU SAURARA : Sanarwan sabuwar Gwamnatin Kano ya janyo cece kuce.
Sabuwar Gwamnatin  Jihar Kano ta Injiniya Abba Kabir Yusif ta fitar da sanarwa ga daidaikun Mutane,  kungiyoyi da sauran  al’umma dake ci gaba da gine gine a wurare mallakar al’umma dasu dakatar da yin hakan.
 An bada sanarwan  Dakatar da duk wani aikin gini a Kan wasu filaye mallakar al’ummar Kano dake Makarantun Jihar Kano, dukkan wuraren ibada, wuraren shakatawa dake sassan Jihar Kano, asibitoci, Makabartu da sauransu.
 Hakazalika ana shawartar Jama’a dasu tsayar da duk wasu rushe rushe da gine gne da ake a dukkan wuraren da asali mallakin Gwamnati ko al’ummar Jihar Kano ne.
 Wannan shawarar an bayar da ita domin amfanin al’umma,  Wanda ta fara aiki daga ranar Alhamis 30 ga watan  Maris Shekara ta 2023 har zuwa wani lokaci, Wanda duk ya saba wannan shawara  Kar ya yi kuka  da kowa face kansa. Kamar Daraktan yada labaran zababben Gwamnan Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya Shaidawa Manema labarai a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *