Zamuyi alfahar da Matasan Nasarawa a fagen wasan kwallon kafa

Zamuyi alfahar da Matasan Nasarawa a fagen wasan kwallon kafa
Ma’azu Maifata.
Daga Zubairu Lawal
Shugaban Qaramar Hukumar Lafia Jagorar Shugabannin Kananan hukumomin jihar Nasarawa Alhaji Aminu Ma’azu Maifata ya bayyana haka bayan kammala gasar kwallon kafa na cin kofin Algon/AA Sule da aka gabatar a filin wasa na Jami’ar Gwamnatin tarayya dake Lafia.
Aminu Maifata yace; yadda matasa suka buga wasa a wannan gasar kwallon kafan ya tabbatar da cewa zasu tsamo kungiyar kwallon kafa ta jihar Nasarawa daga halin da ta fada na fita daga rukunin gasar Primiya ta qasa.
Yace; ba kungiyoyin da suka buga wasan karshe ba. A’a duk kungiyoyin da suka fito daga Qananan Hukumomin 13 sun nuna bajinta. Kuma akwai wakilai da suka sanya ido tun daga ranar da aka fara wannan gasar har zuwa kammala shi, zasu kawo sunayen wadanda suka zakulu musan yadda zamu turasu wasu kungiyoyin na qasa.
Alhaji Ma’azu Maifata yace; mun shirya wannan gasar kwallon kafan ne da hadafin kara zakulo yan wasa a jihar. Da kuma kulla zumunci tsakanin kungiyoyin matasa da zasu san juna suyi abota.
Yanzu abin ya wuce inda muke tsamani munga natijan shirya wannan gasar.
Zamu cigaba da shirya wannan gasar kwallon kafa a duk shekara, saboda wasan kwallon kafa yana cikin tsarin kasuwanci da samar da ayyukanyi da kuma zaman lafiya tsakanin kungiyoyin matasa.
Shima a nasa jawabin Shugaban Qaramar Hukumar Nasarawa Alhaji Muhammad Sani O’otos. Ya bayyana farin cikinsa da matsayin da kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa sukazo wasan karshe.
Yace; munyi nasara a jihar Nasarawa wajen sada zumunta da hadin kan matasanmu a fadin jihar.
Yace; koda bamuyi nasara ba amma fatanmu an tashi lafiya kuma munzo na biyu.
Shugabannin Qananan Hukumomin na jihar Nasarawa sun halarci filin wasa da aka buga wasan karshe tsakanin kungiyar kwallon kafa na garin Lafia da Kungiyar kwallon kafa na garin Nasarawa. Inda Lafia ta samu nasara da ci uku da daya kan Nasarawa.
Kungiyar kwallon kafa ta Lafia ta samu kwaitar kofi da 500,000
Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa ta samu Kofi da 300,000
Kungiyar kwallon kafa ta Karu ta samu 200,000
An fara gasar lafiya an kuma kammala shi lafiya. Shugaban Hukumar Wasannin na jihar Nasarawa Muhammad Alkali (SK). Ya bayyana jin dadinsa da yadda Bangaren Gwamnati suka tsoma hannunsu cikin harkan wasanni a jihar Nasarawa.
Yace; wasan kwallon kafa yana samar da ayyuka yana magance zaman kashe wando ga matasa kuma yana nishadan tarwa. Yanzu Ku duba yadda dubban jama’a suka halarci wannan filin wasan?. Yan nuna jihar Nasarawa suna son harkan kwallon kafa.
Hoto na farko Mataimakn Gwamnan jihar Nasarawa Dr. Emmanuel Akabe yake mika kofi ga kungiyar U-13 na Wamba.
Hoto na biyu
Gwamna Abdullahi Sule da iyalansa wajen bikin rantsarwa karo na biyu
Hoto na uku
Shugaban Qaramar Hukumar Lafia Alhaji Aminu Ma’azu Maifata yake mika kofi ga kungiyar kwallon kafa ta Lafia

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *