Rikici a Majalisan Dokokin Nasarawa  ta yaya  Shugabanni biyu.zasu jagoranci Majalisa?

Rikici a Majalisan Dokokin Nasarawa  ta yaya  Shugabanni biyu.zasu jagoranci Majalisa?
Daga Zubairu Lawal
A ranar talata 6/6/2023 bangarori biyu sun gudanar da zaben Shugaban Majalisan Dokoki a jihar Nasarawa a gurare dabam dabam.
Zaben da yabar baya da kura ya haifar da sabani a tsakanin yan Majalisan a yayin zaben  shugaba kwara daya da zai jagoranci Majalisa na bakwai.
Yan takarar guda biyu suka fito daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar. Duk da cewa yan adawa suke da mafi rinjaye a Majalisan. Kama da PDP da take da membobi 8 SDS 3 NNPP 1
Jam’iyyar APC tana da mambobi 11  cikin 24 yayin da yan adawa suke da mombobi 13.
Shugaban Majalisan Dokokin jihar Nasarawa Hon. Balarabe Abdullahi memba mai wakiltan Umasha Wanda ya jagoranci Majalisan tsawon shekara takwai ya neme komawa a karo na uku.
Shima mai wakiltan Kokona ta yamma Hon. Daniel Ogazi ya fito takarar jagorancin Majalisan.
Tun karfe hudu na asuba wasu yan Majalisan suka kasance a kofar shiga zauren majalisan. Duk da sanarwan da Gwamnatin jihar ta bayar na dakatar da zaben majalisan a ranar talata.
Bangaren Hon. Ogazi ya samu goyon bayan yan majalisa 13 wadanda suka rufa masa baya sukayi zaman dirshen a majalisan.
A bangaren Shugaban Majalisa mai ci Hon. Balarabe Abdullahi akwai membobi 10 da suke kewaye da shi.
Bangaren Hon. Balarabe Abdullahi sun gudanar da tasu zaben ne a Ma’aikatan Kananan Hukumomi da raya Masarautun gargajiya ta jihar. Yayin da suka zabe Hon. Balarabe Abdullahi  da Hon. Kudu a matsayin Shugaba da mataimaki.
Su kuma Bangaren Hon. Daniel Oga Ogazi sun gudanar da zaben su ne a cikin zauren Majalisan Dokoki na Jihar tare da membobi 13. Inda suka zabe Hon Daniel Ogazi  tare da Muhammad Oyanki a matsayin Shugaba da Mataimaki.
Tuni kowani bangare ya rantsar da Membobin Majalisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *