Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya raba tallafin buhu 3,100 ga Talakawa

Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya raba tallafin buhu 3,100 ga Talakawa
Daga Zubairu Lawal
Cikin tallafin da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yake rabawa domin rage radadin talauci bayan cire tallafin man petur da Gwamnatin tarayya tayi.
A ranar Talata Gwamna Abdullahi Sule ya garzaya kananan hukumomin Awe, Keana, da Obi, domin raba tallafi kamar yadda ya fara a ranar juma’a.
Gwamnan ya garzaya kananan Hukumomin uku inda aka rabawa Talakawa marasa galihu tallafin abinci.
Gwamna Abdullahi Sule ya rabawa Talakawa buhuhunan shinkafa 3,100 kuma kowani mutum an hada masa da naira 5,000.
Yace; baya ga wannan tallafin akwai masara za a kawo nan gaba. Wanda bai samu wannan ba, zai iya samun mai zuwa.
An tsara rabon tallafin ne ta zakulo mutani 100 daga kowani gunduma adadin mutunin 1000 ke nan.
Shima a nasa jawabin Sarkin Awe Alhaji Isa Abubakar yayi godiya ga mai girma Gwamna Abdullahi Sule da ya jagoranci rabon tallafin.
Sarkin yace; cire tallafin man petur ya jefa dubban mutani cikin wahala. Amma Allah (T) yace; duk tsanani sauki na nan Tafe.
Yayi kira ga al’umman da suka amfana da wannan tallafin suyi amfani da shi ta yadda ya dace. Kada su sayar kuma kada suyi al’mubazaranci.
Sarkin yayi kira ga al’umman yankin Awe dasu cigaba da zaman lafiya kamar yadda sauka saba.
Tawagar Gwamnan ta garzaya garin Keana da Obi inda a nanma ta raba tallafin buhu 1000 daya daya a kowani Qaramar hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *