Ko KUN SAN- Makabartan dake bukatar tallafi a Nasarawa?

 

Mai Kula da Makabartar Kofar Makama dake yankin karamar Hukumar Lafia Usman Abdullahi ya yi Kira ga Masu hannu da shuni da Gwamnati da su sake Gina katanga da Kuma gwashe sharar da take gefen Makabartar D
dan samar da yanayi Mai kyau.

Mai kula da Makabartar yayi wannan rokon ne a sadda yake Magana da wakilin mu yau a Lafia.

Ya ce biyo bayan Gina kwalbatin kofar Zanwa da Hukumar dake kula da zaizayar kasa NEWMAP ta yi,wasu Al’ummar yankin sun Mai da wani yanki na Makabartar a Matsayin wurin zubar da shara,inda yace akwai bukatar yin roko na ceto Makabartar daga lalacewa.

Abdullahi yace Gina katangar,Samar da wuta da sauran abubuwan more rayuwa a Makabartar zai je nisa ba kusa ba wajen Samar da yanayi Mai kyau ga Mutanen da suke aiki wajen tabbatar da yanayi Mai kyau a makwantan.

Ya bayyana damuwa ta yadda wasu mutane kan saki shanu cikin Makabartar,Malam Abdullahi ya gargadi jama’a su kaucewa wannan dabi”ar.

Mai kula da Makabartar ta Kofar Makama dake nan Lafia yace ambaliyar ruwa ya shafi Makabartar ,ya roki Al’ummar yankin da suka sanar da su akan lokaci a sadda aka samu wani da ya rasa rai saboda yin tuno da wuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *