Gwamnan Nasarawa ya karyata zargin niman taimakon Wike kan shari’ar zabe

Gwamnan Nasarawa ya karyata zargin niman taimakon Wike kan shari’ar zabe
Daga Zubairu .Lawal
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya karyata zargin da Shugaban  jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Nasarawa yayi cewa Gwamnan yana kamun kafa ga ministan Abuja ya taimakeshi kan ahari’ar zaben jihar.
Da yake zantawa da manema Labarai Gwamna Abdullahi Sule ta bakin mai taimakawa kan harkokin yada labarai Kwamared Piter Ahamba yace; san san wannan zargin bata da makama.
Yace; Shugaban Jam’iyyar PDP Hon. Orogu ya rasa abinda zai fadane domin yasan bazasu kai labari a shari’a ba.
Yace; Hon. Orogu yana zargin Gwamna Abdullahi Sule cewa yaje Abuja yana niman taimakon Ministan Abuja Hon. Wike da wasu ministochi su taimaka masa kan shari’ar zaben Gwamnan jihar, to su yan jihar ne ko Alkalaine? Inji Piter Ahamba.
Yace; Gwamnan Abdullahi Sule ya gana da ministan Abuja domin gudanar da wasu ayyukan raya kasa da ta shafi birnin tarayyar Abuja da jihar Nasarawa.
Yace; karamar Hukumar Karu tafi kusa  da birnin tarayya fiye da ko ina a fadin Nijariya.
Kwamared Piter Ahamba yace; Gwamnan Abdullahi Sule mai kishin jihar Nasarawa ne. Saboda haka zai iyayin mu’amala da kowa domin Samar da cigaban jihar Nasarawa.
Mai taimakawa Gwamnan kan harkokin yada labaran ya kalubalanci Shugaban Jam’iyyar PDP da yake cewa babu tsaro a jihar Nasarawa, yace; a duk Arewacin Nijariya inane yakai jihar Nasarawa zaman lafiya?
Kwamared Piter Ahamba yace; samaun zaman lafiya mai durewa a jihar Nasarawa kowa yana barci da ido biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *