Zamu sanya ido kan kotunan shari’a a Nasarawa”

Zamu sanya ido kan kotunan shari’a a Nasarawa”

Kwamishinan Shari’a
Daga Zubairu Lawal
 Attorney General kuma  Kwamishinan Shari’a na jihar Nasarawa Barrister Labaran Shuaibu Magaji  yace; Ma’aikatar Shari’ah ta Jihar Nasarawa  zata rinka sanya ido sosai wajen tabbatar da ana gudanar da shari’o’i cikin hanzari da kuma adalci.
 Zamu sanya ido a kotunan jihar don hana dannewa dan ganin ana gudanar da Shari’a cikin gaskiya da adalci.
 Kwamishinan yace; zamu tabbatar da ana gudanar da  shari’o’in a kotunan jihar domin hana cunkoso a gidajen zaman wakafi na Jihar Nasarawa.
 Barista Labaran Shu’aibu Magaji  ya sanar da haka ne a lokacin daya karbi bakuncin mambobin ‘yan-jaridu na jihar da suka ziyarce shi a ofishinsa dake lafiya babban birnin jihar.
 Yace; Ma’aikatan Shari’ar bazata zura ido ta kyale yadda wasu Alkalai ke yiwa Shari’a hawar qawara ba. Ta hangar daura mara gaskiya kan mai gaskiya ba.
Yace; zasu tabbatar da ana gudanar da Shari’a akan lokaci.kuma ana hukunta mai lefi gwargwadon lefinsa.
Ba zasu yarda a riqa tara Shari’a yana daukar dogon lokaci ba.
Ya kuma yi godiya ga tawagar yan jaridun da suka kawo ziyarar domin hada karfi don aiki tare masamman wajen Shari’a.
Tunda farko Shugaban kungiyar Yan Jaridun manema Labarai na jihar  Nasarawa Kwamared Isa’ac Ukpoju; yace; wannan ziyarar na karfafa dangan taka domin gudanar da aiki tare domin wayar da kan al’umman jihar Nasarawa.
Yace; yan jarida suna da rawar takawa wajen yaki da taimakawa jihar tare da fahintar da al’umman jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *