Za’ayi gwanjon gawawakin mutum tara Asibitin FMC Keffi dake Nasarawa 

Za’ayi gwanjon gawawakin mutum tara Asibitin FMC Keffi dake Nasarawa 
Daga Zubairu Lawal
Hukumar Asibitin Gwamnatin tarayya dake garin Keffi(FMC) ta baiwa Hukumar kula da dalubai masuyiwa kasa hidima ( NYSC) wa’adin sati biyu su kwashe gawawakinsu guda tara dake dakin ajiyar gawawaki na Aaibitin ko kuma tayi masu zana’idar bai daya.
Da take magana ga manema Labarai Jami’ar yada Labarai na Asibitin Miss Esther Bature tace; wannan umurnine daga hukumar gudanarwa na Asibitin dake garin Keffi cikin jihar Nasarawa.
Tace; Asibitin ta dauki wannan matakin ne sakamakon dadewa da gawawakin sukayi ba tare da masu Gawawakin sunzo sun biya kudi sun kwashe su ba.
Tace gawawakin adadinsu ya wuce  wata shida, sharudan ajiyar gawa.
Tace; gawawakin mutum tara(9) za tayi gwanjon zana’idarsu a rami daya matukar basu zo sun kwashe ba.
Adadin ajiyan gawa a Asibitin baya wuce wata shida. Amma wadanan sun kwashe shekaru har yanzu masu gawar basu halarci Asibitin domin daukar gawawakin su ba.
Tace; ko iyalan wadanan daluban sun San da cewa ya’yansu sun mutu gawawakin su na Asibitin Gwamnatin tarayya dake garin Keffi? Wato ( Federal Medical Centre). Ko basu sani ba oho.
Abin al’ajabi wasu gawawakin tun a shekarar 2021 suke ajiye a Asibitin. Wasu kuma tun a ahekarar 2022 har yanzu babu wanda yayi cigiyarsu.
 
Tace; wannan wa’adin na sati biyu zai farane daga yau Juma’a 22/9/2023 Dan haka masu gawawakin su gaggauta zuwa su biya kudi su kwashi gawawakin su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *